𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣1️⃣
........Tana fitowa ɗauke da dankali ya fuske kamar bashi ba ya cigaba da game ɗin yana satar kallonta ta gefen ido. Ganin ta fara firar dankalin ya sashi ajiye wayar tasa a table ɗin ya miƙe, gefenta ya tsaya kaɗan, ya ɗauka wuƙar data ajiye saman chopped board ya fara yanka wanda ta fere, bata kulashi ba, ba kuma tayi magana ba ta cigaba da ferewa tana ajiye masa. Shima sai baiyi magana ba ya cigaba da yankawa, idan ya ɗan tara sai ya zuba a cikin ruwan data ajiye a bowl. A haka har suka kammala, kasancewar ta rigashi gamawa ita ta fara barin wajen ta ɗakko preyn fan ta dawo inda yaken ta zuba ruwan sabulu kaɗan ta wankesa da soso ta ɗaureye duk yana satar kallonta. Komawa tai gaban gas ta kunna ta ɗora sannan ta zuba man data ɗakko. Dai-dai nan ya kammala, sai ya wanke mata dankalin ya sake masa ruwa ya tace sannan ya juyo yana miƙa mata robar. Sai da ta hararesa ta amsa, shi dai ya gimtse dariyarsa da ƙyar ya juya yana ɗauraye wuƙa da sauran abinda sukai amfanin. Lulu kam koda albasanta ya soyu ta zuba dankalin sai ta nufi frizzier, kifi tai ƙoƙarin cira sai dai sanyin da ya ratsa mata hannu ya sata faɗin, “Ouchh!!”. Juyawa yay yana kallonta, ganin yanda take yarfe hannun ya sashi nufarta, hannun ya riƙo ya saka cikin nashi ya rumtse ɗumin nasan ya ratsata, sai kuma ya jawota gaban fanfo ya kunna ruwa ya ɗauraye mata hannun, sannan ya jawo ƙaramin towel ya saka mata hannun ciki. Komawa yay ya ciro kifin har biyu masu ɗan girma ya dawo ya wanke su sannan ya dubeta, ɗauke kanta tai da ga kallon gefen ido da take masa. Shiko da ba lura yay ba ya ce mata “Yankawa zakiyi?”.
Ƙaramar harara ta sakar masa da tura baki gaba sannan tace e.
“Kai dai Aliyu kana shan harara wlhy abin tausayi”. Ya faɗa yana yanka kifin. Hararar tasa ta sake yi da matsawa gaban dankalinta ta da ke cikin mai......
Kusan a tare sukai aikin, sai dai itace ke girkin shi kuma yana taimaka mata da yanka miƙo, duk da dai ba itace ke cewa yayi ɗin ba. Ya shiga matuƙar mamakin ganin yanda take girkin dama yanda tayisan, dan harga ALLAH bai kawo ta iya abinci ba. (Sai dai abinda Smart bai sani ba girki yana cikin hubby ɗin Lulu, tana son girki kuma ta iya kalolin girki na zamani sai dai fa sai ta gadamar yi take yin, tamafi sakin jiki tayi idan taje gidan Dada (kakarta matar Alhaji Garko) amma idan kaga tai girki a gidansu ko gidan Uncle Yousuf lallai ƴan arziƙinne a kanta ko taso yima Daddy wani bazata ko Uncle Yousuf ɗin). Abinda tai ɗin ya sashi jin daɗi bai ji ƙyashin tayata suka gyara kitchen ɗin ba duk da ma ba wani ya ɓaci bane dan Lulu akwai iya ƙwaf-ƙwaf ɗin aiki komai aka taɓa ana wankesa ne da zarar an gama da shi, inda ko ruwa ya taɓa za'a goge, tana hakanne kuma saboda yanayin tsaftarta, hakan kuma sai ya sake bama Smart nutsuwa kasancewarsa mutum mai shegen tsantseni da tsantsami. Dining takai komai ta ajiye tai wucewarta bedroom batare da ajiye plate ko kofin da za'ayi amfani ba. Baiyi magana ba saboda kiran Uncle Yousuf da ke shigo masa. Kiran ya amsa ya koma falo ya zauna. Har ya kammala wayar bata fito ba, dan haka ya miƙe yabi bayanta. Samunta yay kwance a kan gado rufda ciki sai dai ta canja kayan jikinta zuwa wasu, a hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da yin gyaran murya. Kamar bazata kulashi ba sai kuma ta buɗe idanun kaɗan a kansa. Cikin ido suka kalla juna, ta janye nata da wani yin gaba da lips kamar mai son yin zinɗe, ta ce, “Wlhy in ma da wani abun kazo bazanyi ba na gaji”.
Dariya taso bashi dan yanda tai maganar da iyakar gaskiyarta, amma sai ya dake da ƙyar ya ce, “Ni na isa na sake saka Madam aiki ai tsaurin idon nawa ma sai yayi yawa. Sannu nazo yi miki, da kuma ban haƙiri da bikon kizo kici abinci. Har dama tausa idan kina so ƙyauya”.
Cikin taɓe baki da harararsa akan zancensa na ƙarshe ta ce, “Kai ne handin burum kaje kaita ci”.
“To Aliyu Hydar ka ƙara samun cigaba kenan, da ga illiterate velleger ka koma Maye, yau kuma handin burum, ɗan Ammah baban Ammah mijin Mawadda....”
Filon da take kwance ta fisga kafin ma ya kai ƙarshen sunanta da taji ya kamo ta wulla masa. Da sauri ya cafe yana zaro idanu, ya ce, “Madam ina rabaki da halin jifar nan kar wataran ki ɓazge min hanci kamar yanda Iffah tai ma Uwa fa tom”.
Wasu ta sake fisga tana tashi zaune ta cigaba da jefa masa su, tun yana karewa har ya fita yana dariya dan ya kula dai fushin ake saukewa a haka. Ƙwafa tayi itama da ballama ƙofar harara kamar itace tai mata laifin.....
Shi da kansa ya ɗebo plates ɗin da spoons bayan ya wanke su, ya zauna a ransa yana faɗin (Bari muci girkin ƴar madara muji). Da tea ya fara, lokacin da ya kai dankali da source ɗin ƙwai bakinsa sai da ya lumshe idanunsa. Wannan fa shi ake kira kama da wane bata wane, UBANGIJI mai rahama. UBANGIJI mai jin ƙai da baya haɗama bawa zafi biyu, idan ya jarabceka ta nan sai ya sauƙaƙa maka ta can dan kaji sanyi. A duk inda kaga mutum da halayya mara ƙyau kar ka yanke masa hukunci da ɗari bisa ɗari ɗin munanan ayyukansa, UBANGIJI shine kaɗai yasan abinda ke cikin zuciya da sirrikan ɓoye ga bayinsa. Ita dai a zahirinta duk wanda ya ganta suna ɗaya zai bata, amma a baɗininta sai UBANGIJIN da ya halicceta ya san kayarsa, sai ko wanda ya ƙaddara ya santan kamar dai shi mijinta a yanzun...
Yana gab da kammalawa ta fito, sai dai yitai kamar bata gansa ba ta zauna a falo ta ɗauka laptop ɗin ta ta cigaba da aikinta na ɗazun batare da kallon ko inda yake ba ko sau ɗaya. Shi ko dai sai satar kallonta yake time to time. Koda ya kammala sai ya ɗibo farfesun kifin cikin dauriya dan baya son kifi shi sam da tea ya nufota, ƙaramin coffee table ya jawo gabanta ya ajiye, ƙamshin kifin ne daya dakar mata hanci ya sata ɗagowa, harararsa tai ƙoƙarin yi yay saurin faɗin, “Ni dai tausaya min da hararar nan gidan ma zan bar miki karki lashe ni Ammah ko yaye ni batai ba”.
Hararar tasa dai tai ta ɗauke kai, sai kuma ta sake ɗagowa ta dubesa, karan farko ta saki murmushin da ke bayyana beauty point ɗinta da farare haƙoranta, ga wanda ya santa a kallo ɗaya zai fahimci na mugunta ne, saboda bata murmushi sai ta so, wanda kuma bai santa ba zai ɗauka yinsa matsayin birkita kwanyar duk wanda ya kalletan ne. Girarta a sama ta ce, “Waye zai fitan? Ka manta yau a gidan nan babu shiga babu fita? Ai duk yanda ka dama haka kowa zai sha wlhy. Ta miƙe ta nufi hanyar bedrooms. Da kallo kawai ya bita na mamakinta ne ko na son ƙarin bayani akan maganar tata ne oho masa. Yana a wajen harta da dawo da keys a hannu, a kallo ɗaya ya gane na ƙofar falon ne da ƙofar kitchen ta baya. Sai da takai zaune sannan ta tura su cikin rigarta a gaban idonsa ta gyara tana ɗaukar tea ɗin da ya ajiye mata ta kai baki.
“Idan ma wasa kike ki daina. Uncle Yousuf fa ke jirana tare da Yaya Abdull-Hameed”.
“Oh really?”.
Ta faɗa cike da rainin wayo. Hannu ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya kai zaune a kusa da ita cikin lallashi ya ce. “Mawaddat Please seriously wlhy jirana akeyi, babu jimawar nan yay kirana kuma important ne zuwa 12”.
Batama ko kallesa ba balle ta tanka masa, sai ma kifinta data fara ci a hankali tana wani lumshe idanu taba banza ajiyarsa. Rasama mi zaiyi yay, cikin son ta fahimta yay ƙoƙarin kamo hanunta ta balla masa harara. “Karka kuskura hannunka ya kai jikina. Ka kuma kiyayi yin hakan inba haka ba kasha mamakin sanin ainahin Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. Kasan bazaka iya ƙarasa wasan ba miyasa ka fara? Common ƙyaleni bana buƙatar hayaniya, ba kace da ni zaka buga game ba? Muje zuwa”.
(Tana mun magana kamar wata lady boss) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam kansa kawai ya dafe. Abu tamkar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa har 12 tayi Lulu bata da niyyar bama Smart key ɗin nan, zuciyarsa na raya masa ya turmuzeta ya amsa amma yana gargaɗin kansa karta tada masa aljanu, dan yasan mata da iya aljanu. Sha biyu da kusan kwata kiran Uncle Yousuf ya shigo masa. Ya ɗaga ya gaida shi da mutuntawa kamar yanda ya saba. Da ga can Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu yaya dai? Kai muke jira na ga har 12:15?”.
Ɗan kallon Lulu da ke ta aikinta a laptop tana zuba murmushin mugunta yayi, a can ƙasan maƙoshi ya ce, “Uncle ta kwashe keys ɗin ne fa, wai tunda na hanata fita nima babu inda zanje”.
“What! Mawaddat ɗin? Kaga bata wayar Please bana son shiririta”
Maimakon bata sai ya saka a hansfree yanda zataji, kiran sunanta da Uncle Yousuf ɗin yay ya sata ɗagowa ta kalla wayar, sai kuma ta amsa da “Yes Papa good afternoon”.
“Afternoon Dear. Miya faru kika hana Aliyu fitowa ga shi munata jiransa?”. Murmushin muguntar da take ta faman yi tun ɗazun alamar duniya ta mata daɗi ta sake saki da faɗin, “Uncle You shi ya zaɓi hakan ai, dan haka ka manta da shi kawai, dan yanda ya hanani fita sai dai mu yini tare a gidan.”
“Mawaddat Please!!”
“Uncle please”.
Ta faɗa itama kamar yanda yayin tana tura baki. Kai kawai Uncle Yousuf ya dafe da ga can, yayinda Coach ke kwasar dariya dan Smart ɗin kawai ya ke hangowa, kai mace daban ce, yo inba mace daban take ba Smart ɗinsa ne da ya sani mai tsaurin nan da rashin son magana za'a kullema ƙofa a hanashi fita. Aure aunre yayi. A ɓangaren Uncle Yousuf kam iyakar lallaɓa yay ma Lulu tafa ce ba gudu babu ja da baya, har ya koma faɗa amma tai biris, ba komai ke tunzurata ba kuma sai ganin yanda fuskar Smart ta fara canjawa da dauriyar da yake zuwa ɓacin rai. “Uncle bye”. Ta ce cikin siririyar dariya tana miƙewa tare da laptop ɗinta da wayoyinta tabar falon ma tana ɗagawa Smart yatsu biyu na ƙularwa ta ce, “2-1 ka shirya yin game over gaba kaɗan”.
Wani irin bahagon iska ya furzar da ga bakinsa yana mai dafe kansa. Da ga can cikin tunzura shima Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu wai yarinyar nan tafi ƙarfinka ne da karɓar key a wajenta ya gagareka. Be a man mana Son”.
“Uncle bazaka gane bane wlhy, yarinyar nan azababbiya ce, tafa saka key ɗinne.....”
Sai kuma yay shiru fahimtar ɓaranɓaramar da yake neman yi. Uncle Yousuf zai sake magana coach ya katsesa da faɗin, “Kaga ƙyaleta muje mu samesa a can kawai nikam, dan amarya dai bata laifi koda ta kashe ɗan masu gida. Zakina jiramu karka damu”.
Kafin Smart ya ce wani abu an yanke wayar, sai kawai ya girgiza kai. Wannan ma sauƙin kan na Coach ya sa yake sake jin ƙaunarsa a ransa. Mutumin nan shi na musamman ne a garesa, dan ya taka rawa kala-kala a cikin rayuwarsa da har abada bazai manta ba........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-*
COMMENTS